Shugaban ya kuma ce zaman al’umar kasar tare na da matukar muhimmanci saboda ba a iya misalta alfanun zaman lafiya tare, duba da yadda ‘yan kasar ke tabuka abin a zo a gani tare, idan suka hada karfi wuri guda.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin taron karawa juna sani na jigon jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmad Tinubu karo na 12 da aka saba gudanar duk shekara da aka gudanar a jihar Kano.
Buhari ya kara da cewa, duk da rikice-rikicen kabilanci da ake samu lokaci-lokaci a tarihin Najeriya, ya na da yakinin cewa, ‘yan kasar sun yi imani kan cewa, duk da banbance-banbancen addini, al’ada, yare, 'yan kasar na kaunar juna kuma sun fi karfi tare.
Ya kara da cewa 'yan kasar su rinka duba albarkatun da Allah ya ba kasar tare da ganin alamomin zaman lafiya da hadin kan kasar a yanayim da ake ciki.
Shugaba Buhari wanda ya halarci taron ta yanar gizo don murnar cikar shekara 69 a duniya da murnar zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya yaba da kokarinsa na neman hadin kan kasa a koda yaushe.
Daga karshe, shugaba Buhari ya bayyana cewa, a matsayin dan gwagwarmayar siyasa, jigo a jam’iyyar APC, abokin aiki, mamba a majalisar ministocinsa, ko a mai ba shi shawara, Bola Tinubu, ya yi namijin kokari, kuma a ko da yaushe ya na yin duk mai yiwuwa wajen ci gaban Najeriya a matsayin kasa dunkulalliya.