Gwmantin Turkiyya tana ta yin sintiri a yankin da ba a yakin ne don ta kawar da mayakan Kurdawa daga kan iyakarta.
Turkiyya ta na daukar mayakan Kurdawan Syria a matsayin ‘yan ta’adda da su ke da alaka da mayakan Kurdawa na Turkiyya, wadanda su ka yaki gwamnatin Turkiyya na tsawon shekaru 30, amma Kurdawan Syria kuma su na daga cikin muhimman kawayen Amurka a fadan da ake yi da ‘yan tada kayar baya na kungiyar ISIS a Syria.
Sai dai dakarun da ke karkashin jagorancin Kurdawan sun janye daga wurin kamar kilomita 14 daga iyakar kasar, amma Turkiyya ta na kira da su matsa kilomita 30. To dai har yanzu ba a tsai da shawara kan cikakken bayanan fadin yankin da ba a yaki a cikin din ba, da kuma wanda yake da iko da shi.
A shekaru hudu da suka gabata, dakarun Amurka sun samar da zaman lafiya tsakani sojojin Turkiyya da kuma mayakan Kurdawa.