Ba Da Gangan Ake Rike Da Kudaden IPMAN Ba – Hukumar NMDPRA

Karancin Man Fetur Ana Daf Da Bukukuwan Kristimeti, Sabuwar Shekara - Masu Ruwa Da Tsaki

A daidai lokacin da karanci da tsadar man fetur ke kara kamari a kusan dukkan sassan Najeriya, an sami sabani da ka iya tsananta matsalar tsakanin bangarorin da lamarin ya shafa, kamar kungiyar ciyamonin depot-depot na IPMAN, kamfanin NNPCL da ma hukumar NMDPRA.

Batun karanci da tsadar mai abu ne da ya kara tsananta musamman a farko-farkon makon da ya gabata, inda ake fama da dogayen layuka a gidajen mai a sassa daban-daban na kasar, lamarin da ya rikide zuwa tashin farashin man kuma rahotanni sun yi nuni da cewa a Sakkwato, Kaduna, da Kano ana sayen kowacce lita a gidajen mai daga naira 900 sama, ‘yan bumburutu kuma na saida wa a kan kusan dubu 2.

Shugaban kungiyar IPMAN reshen Jihar Zamfara, Alhaji Surajo Yahaya Kamba, ya ce kin biyan hakokkinsu ne sanadiyar matsalar tsada da karancin da ake ciki kuma muddin ba’a biya su ba, zasu dauki tsauraran matakai na gaba.

Matsalar man fetur a Najeriya

A nasa bangaren, shugaban hukumar kula da dokokin fannin albarkatun man fetur na kasa wato NMDPRA, Mallam Faruk Ahmed, ya ce lallai hukumarsa na bin kungiyar IPMAN da wasu dilallan man fetur bashi, amma ba da gangan suka rike kudaden ba, su ma suna bin wasu bashi, kuma a yanzu za’a biya karin naira biliyan 10 a cikin bashin na IPMAN, amma sai in an biya hukumar NMDPRA sannan ita ma ta sami damar sauke nata nauyin.

Bangaren IPMAN dai ta nuna shakku a kan ikirarin kamfanin NNPCL na cewa akwai wadataccen man fetur a cikin kasar, sai dai kamfanin NNPCL ta bakin babban daraktan yada labaransa Olufemi Soneye, ya sake jaddada cewa babu matsalar wadataccen man illa matsalar dako.

A ranar Talata an sayar da kowacce litar mai tsakanin naira 850 zuwa naira 900, a yayin da ‘yan bumburutu ke sayar da nasu a kan Naira dubu daya da dari uku zuwa naira dubu da dari hudu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, duk kokarin ji ta bakin kamfanin NNPCL kan cece-kuce a kan wadatar mai dai ya ci tura.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Da Gangan Ake Rike Da Kudaden IPMAN Ba – Hukumar NMDPRA