WASHINGTON DC - A yau Talata, Majalisar Wakilan Najeriya ta zaratar da kudiri akan gayyatar Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur(mai kula da fetur), Heineken Lokpobiri da takwaransa Mai Kula Da Iskar Gas, Ekperikpe Ekpo game da matsalar karancin man da ake fama da ita a kasar nan.
Har ila yau Majalisar Wakilan ta gayyaci shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, akan matsalar karancin man a kasar.
Majalisar na sa ran ministocin da shugaban kamfanin mai na NNPCL suyi mata bayani game da asalin dalilan da suka sabbaba karancin man da kuma matakan da za’a dauka wajen shawo kan matsalar.
Saidai ba’a tsayar da ranar ganawar ba.
A makon daya gabata dogayen layukan ababen hawa suka sake bayyana a gidajen man kasar nan, inda matsalar ta cigaba har zuwa wani sabon makon inda masu ababen hawan da suka matsu ke sayen litar man akan naira 800 a gidajen mai, a yayin da ‘yan bumburutu ke sayarwa akan naira 1, 500.
Dandalin Mu Tattauna