Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsada Da Karancin Man Fetur Ya Ta'azzara A Arewcin Najeriya


Farashin Man Fetur Ya Tashi Sakamakon Janye Tallafin Man Fetur
Farashin Man Fetur Ya Tashi Sakamakon Janye Tallafin Man Fetur

‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da yadda karancin man fetur da kuma tsadarsa ta mamaye arewacin kasar, bisa yadda al’umma ke shan wahalar samun wannan makamashi da rayuwa ta dogara da shi. Yanzu haka farashinsa ya yi tashin gwauron zabi ya wuce farashin gwamnati.

Dogayen layukan ababen hawa a gidajen Mai na kara tsammari a arewacin Najeriya, lamarin da ya janyo tashin farashi, amma duk da haka wasu ‘yan Najeriya sun shafe tsawon lokaci a dogayen layin dake gidajen Mai.

Alhaji Bashir Salisu shine shugaban dillalan Man-fetur ta IPMAN reshen Arewa maso yammacin Najeriya, wakiliyar Sashen Hausa ta tambayashi ko menene musabbabin yawaitar karancin man fetur a arewacin Najeriya har ma da Abuja.

A hirarsa da Muryar Amurka, Aliyu Usman Jibo Masanin tattalin arziki kuma Malami a makarantar koyar da Malamai dake Jihar Jigawa ya ce “halin da ake ciki na karancin Man Fetur a Najeriya ka iya shafar harkokin yau da kullum, wanda kuma ka iya shafar tattalin arziki.

Muryar Amurka ta yi kokarin tuntubar kamfanin Albarkatun Mai na kasa, NNPCL, sai dai basu amsa ba, har izuwa hada wannan rahoto.

Domin karin bayani saurari rahotan Ruƙaiya Basha.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG