Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yayin Da Karancin Man Fetur Ke Kara Kamari A Jihohin Najeriya, Dillalan Mai Na Cewa NNPCL Baya Samar Musu Da Man


Layin neman Mai a Yola
Layin neman Mai a Yola

Dillalan mai a Najeriya sun dora alhakin karancin fetur na baya-bayan nan akan tsarin da babban kamfanin man fetur na kasar, NNPCL, ke bi wajen samar musu da shi.

WASHINGTON DC - Shugaban kungiyqar mamalaka gidajen mai na najeriya PETROAN, Billy Gillis Harry, ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin sassafe na tashar talabijin ta Channels mai suna “Morning Brief” a turance.

A Alhamis data gabata, mai magana da yawun kamfanin nnpcl, Olufemi Soneye, yace “karancin man fetur din da ake fama da shi a wasu sassan kasar nan ya samu asali ne daga matsalolin tsare-tsare kuma an riga an magance su”.

NNPCL ya kara da cewar farashin albarkatun man fetur ba zasu sauya ba sannan ya bukaci ‘yan Najeriya da kada suyi kokarin boye man kasancewar akwai wadatarsa a fadin najeriya.

Saidai, shugaban kungiyar mamalaka gidajen man fetur na Najeriya, Billy Gillis Harry, yace ba’a kai ga warware matsalar ba duk da cewar ya yaba da kokarin NNPCL na warware kalubalen.

Karancin fetur na baya-bayan ya kassara dimbin harkokin tattalin arziki a fadin tarayyar kasar sakamakon dawowar dogayen layuka a gidajen man Najeriya.

Matsalar karancin man ta baiwa ‘yan bumburutu damar sayar da litar man naira 2, 000 a wasu jihohin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG