WASHINGTON DC - Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya bayyana cewar matsalolin tsare-tsare ne suka sabbaba dawowar dogayen layukan mai a wasu sassan kasar.
Saidai sanarwar da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar tace, an warware matsalar.
Sanarwar tace, “babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, na so ya bayyana cewar matsalolin tsare-tsare ne suka sabbaba matsalar karancin man fetur da ake fama da a wasu sassan kasar nan a halin yanzu, kuma an riga an magance ta.
“Kuma kamfanin yana son jaddada cewar farashin albarkatun man fetur na nan a yadda suke basu sauya ba.”
Don haka NNPCL na kira ga ‘yan Najeriya dasu kaucewa dabi’ar boye man, kasancewar akwai wadatarsa a kasar”.
Dandalin Mu Tattauna