Dan takarar jam’iyyar Leba Gbadebo Rhodes-Vivour, wanda ya zo na biyu da Abdulazeez Adediran wanda aka fi sani da Jandor na jam’iyyar PDP, wanda ya zo na uku, sun kalubalanci zaben Sanwo-Olu bisa zargin tafka magudi, da rashin bin doka, da rashin cancanta.
Masu kalubalantar zaben Sanwo Olu Sun dogara da cewa Mataimakin Gwamnan Sanwo Olu, wanda ake zargin ke da takardar zama dan kasar Amurka, bai cancanci tsayawa takara ba, don haka nadinsa na mataimakin gwamna ya saba wa doka.
Sun kuma yi zargin cewa nadin nasa ba bisa ka’ida ba ya shafi cancantar gwamna Sanwo-Olu, don haka ya kamata kotu ta soke shigarsu takarar gwamna.
Sai dai kotun kolin da kotun daukaka kara a cikin hukuncin da suka yanke sun yi watsi da kararrakin biyun saboda rashin tabbatar da zarge-zargen da aka yi a cikin koken masu shigar da karar kalubalancin.
Kotun koli a hukuncin da ta yanke, ta ce ba ta sami wani kwakkwaran dalili na kaucewa hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe da na daukaka kara suka yanke ba na cewa an zabi Sanwo-Olu a matsayin gwamnan jihar Legas bisa doka a baya ba.
Kotun Daukaka Kara a cikin hukuncin da ta yanke a watannin baya ta ce samun shedar zama dan kasar waje wanda ake zargin mataimakin gwamnan Sanwo-Olu, bai hana kowanne dan asalin Najeriya tsayawa takara ba.
Mai shari’a Lawal ya bayyana cewa sharadi daya tilo da dan Najeriya mai shedar zama dan kasa biyu zai iya rasa ‘yancinsa na zabe a matsayin gwamna idan ya fita a hukumance cewa shi ba dan Najeriya bane.
Daga bisani kotun kolin ta yi watsi da kararrakin guda biyu saboda rashin cancanta.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 762 da 134 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Gbadebo Rhodes-Vivour, wanda ya samu kuri’u dubu 312 da 329, inda Jandor ya zo na uku da kuri’u dubu 62 Da 449.
Hakazalika, Kotun Kolin ta ta tabbatar da nasarar gwamnonin jihar Zamfara, Filato, Ebonyi, da Bauchi a matsayin wayanda suka lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.
Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Dauda Lawal A Matsayin Gwamnan Zamfara
Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da zaben Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Zamfara.
Kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke inda ta bayyana zaben gwamna jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba, sannan ta bayar da umarnin a sake zabe a kananan hukumomi uku na jihar.
A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta soke zaben Lawal da wannan hukuncin nata.
Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta ayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.
Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya sami gagarumin nasara da ya kawar da gwamna mai ci a lokacin Bello Matawalle na jam’iyyar APC, inda ya sami kuri’u dubu 377 da 726 kuma abokin hamayyarsa Bello Matawalle ya sami kuri'u dubu 311 da 976.
Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Nwifuru A Matsayin Gwamnan Ebonyi
Har ila yau, kotun koli ta tabbatar da nasarar Francis Nwifuru na jam’iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar Ebonyi.
Kotun kolin ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara da ke Legas, inda ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Chukwuma Odii ya shigar kan rashin cancanta.
A watan Nuwamban da ya gabata ne kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Nwifuru a matsayin zababben gwamnan jihar Ebonyi a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Tawagar kotun mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Jummai Sankey, a hukuncin da ya yanke, ta yi watsi da karar da Odii ya shigar kuma ta amince da hukuncin da karamar kotun ta yanke a baya amma dan takarar na PDP ya garzaya gabanta don neman a soke zaben na Nwifuru.
Kotun Koli Ta Soke Hukuncin Korar Mutfwang, Ta Tabbatar Da Shi A Matsayin Gwamnan Filato
Haka kuma Kotun koli ta soke hukuncin korar Caleb Mutfwang na kotun daukaka kara, inda ta tabbatar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar Filato.
A ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2023 ne kotun daukaka kara dake da zama a birnin tarayya Abuja ta kori Mutfwang a matsayin gwamnan jihar Filato.
A waccan lokaci kotun daukaka karar ta ce jam’iyyar PDP ta karya dokar kotu tare da bayar da umarnin a gudanar da sahihin zaben fidda gwani a kananan hukumomi 17 na jihar Filato sakamkon yadda kotun ta ce jam’iyyar PDP ta gudanar da taron nata ne a kananan hukumomi biyar kacal na jihar, wanda ya kai ga soke zaben.
Sai dai tawagar masu shari’a 5 karkashin jagorancin Mai Shari'a Emmanuel Agim ya sauya hukuncin kotun daukaka kara da cewa ya sabawa shari'a saboda batun zaben fidda gwani da ya samar da Caleb Mannaseh Mutfwang a matsayin gwamnan jihar Filato ba hurumin karamar kotun bane