Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Tayi Watsi Da Karar Da Aka Daukaka Kan Gwamna Hycinth Alia Na Jihar Benue


Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia
Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da aka daukaka akan Gwamnan jihar Binuwai, Hyacinth Alia ta kuma tabbatar da zaben malamin adinin daya rikide zuwa dan siyasa.

Hukuncin Kotun Kolin ya biyo bayan janye karar da lauyan jam’iyyar PDP, Titus Uba ya yi wacce ta kalubalanci nasarar da Alia na jam’iyyar APC ya samu.

Kawo yanzu, Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara ta Abuja, sun tabbatar da Zaben Hycinth alia a matsayin Gwamnan Benue, sakamakon ayyana shi da Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan daya gudana a ranar 18 ga watan Maris din shekarar 2023.

Haka kuma, kotun tace ya kamata lauyan ya gabatar da zargin yin takardun bogi da ake yiwa Mataimakin Gwamna, Sam Ode, a gaban babbar kotu.

Ta ci gaba da cewar, Uba ya gaza tabbatar da zargin yin takardun bogin akan Ode ta yadda zai gusar da duk wani shakku.

A ranar litinin, dan takarar jam’iyyar PDP ya gabatar da batun a gaban Kotun Koli, inda kotun tayi watsi da karar da aka daukaka tare da tabbatar da zaben Alia.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG