Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Umo Eno A Matsayin Gwamnan Akwa Ibom 


ABUJA: Kotun kolin Najeriya
ABUJA: Kotun kolin Najeriya

Kotun koli dake da zamanta a birnin tarayyar Najeriya, Abuja, ta tabbatar da Umo Eno na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Akwa Ibom bayan ta yi watsi da karar da jam’iyyu uku suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023. 

Wannan hukuncin na zuwa ne biyo bayan da tawagar masu shari’ar kotun koli, karkashin jagorancin mai shari’a Uwani Abba-Aji ta yi watsi da karar da jam’iyyun APC da YPP wato Young Progressives Party da kuma Action Alliance wato AC suka shigar a bisa rashin cancantar Umo Eno ya zama gwamna saboda zargin mika takardun kamalla karatu na bogi, wanda gwamnan ya musanta.

A baya dai, kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da ya yi watsi da karar da ke kalubalantar zaben fidda gwanin da ya gabatar da Umo Eno a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a jihar ta Akwa Ibom.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Okon dai ya bukaci kotu da ta haramtawa Eno takara bisa zarginsa da yin jabun takardar shaidar kammala jarabawar kammala karatun sakandare wato WAEC wadda ya mikawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC domin gudanar da zabe.

Kotun daukaka kara dai ta yi watsi da karar ne saboda rashin cancanta sannan ta ci tarar wanda ya shigar da karar zunzurutun kudi har naira miliyan 15.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa hujjojin Okon sun ta’allaka ne da zato kuma ya kasa tabbatar wa kotu cewa takardun shaidar Eno na jabu ne.

Haka zalika a ranar Talata ma sai da kotun koli ta jingine karar kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yi na soke zaben gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato.

A yanzu dai ‘yan Najeriya na dakon hukuncin kotun koli a zaben gwamnoni 7 a gobe juma’a ciki har da na jihar Kano tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP da Yusuf Nasir Gawuna na jam’iyyar APC.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG