Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Zata Yanke Hukunci Mako Mai Zuwa Kan Zaben Jihar Filato


Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Kotun kolin Najeriya ta jingine hukunci a karar da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya shigar inda ya bukaci ta tabbatar da zabensa.

PLATEAU, NIGERIA - Gwamnan ya yi zargin cewa kotun daukaka kara ba ta yi masa adalci ba, kan matakin da ta dauka na soke zaben nasa.

A ranar 19 ga watan Nuwamba Kotun daukaka kara ta kori gwamnan tare da bayyana ‘dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nentawe Yilwatda a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gwamna Caleb Mutfwang, da bai amince da hukuncin kotun daukaka karar ba, ya bukaci kotun kolin ta ayyana shi a matsayin gwamna.

Mutfwang ta bakin lauyansa Kanu Agabi (SAN) ya ce batu guda daya ne kotun daukaka kara ta duba, daga cikin ababe takwas da suka gabatar a gabanta. Ya ce hukuncin kotun daukaka karar ya saba wa umurnin kotun koli, cewa ya kamata kotuna na tsakiya su duba dukkan batutuwan da aka gabatar a gabansu.

A lokacin sauraron karar a jiya Talata, rukunin mutane biyar na Kotun kolin karkashin shugabancin mai shara’a John Okoro sun saurari muhawara tsakanin dukkan bangarorin lauyoyin dake cikin shari'ar.

Bayan jayayya mai tsanani tsakanin lauyan Caleb Mutfwang, Kanu Agabi, da lauyan Nentawe Yilwatda, J.O Olatoke, kotun kolin ta ce za a sanar da ranar hukunci ga wadanda suke cikin karar. Amma kafin jingine hukuncin, Kotun kolin ta gabatar da tambayoyi biyu masu muhimmanci game da ko kotun sauraren kararrakin zabe tana da ikon saurarar batutuwan da suka shafi jami’iyya.

Kotun kolin ta ayyana ranar 16 ga Janairu a matsayin ranar da zata yanke hukunci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG