Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Kotun Koli Za Ta Yanke Hukuncin Jihohi 7 Ranar Juma’a


ABUJA: Kotun kolin Najeriya
ABUJA: Kotun kolin Najeriya

Kotun Kolin Najeriya da ke zamanta A babban birnintarayya, Abuja, za ta yanke hukunci kan kararrakin gwamnoni bakwai a ranar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024, wanda zai fara da karfe 9 na safe.

Kotun Kolin Najeriya da ke zamanta A babban birnintarayya, Abuja, za ta yanke hukunci kan kararrakin gwamnoni bakwai a ranar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024, wanda zai fara da karfe 9 na safe.

Jihohin da kotun koli zata yanke hukunci akan su sun hada da Legas, Kano, Zamfara, Plateau, Ebonyi, Bauchi, da jihar Cross River.

Yusuf da Gawuna:

A karshen watan Disamba ne dai kotun kolin kasar ta ajiye hukuncin da ta yanke kan karar da gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya shigar gabanta na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da kotun sauraron kararrakin zabe, wanda ya kai ga tsige shi daga mukaminsa.

Kwamitin alkalan mai mutane biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ya yanke hukumcin hakan ne bayan da bangarorin suka gabatar da takaitaccen bayani a kan muhawararsu.

A watan Satumba ne dai kotun ta soke nasarar Yusuf a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, inda ta tabbatar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Kotun daukaka kara ta amince da hukuncin ne a ranar 13 ga watan Nuwamba, inda ta ce takarar Abba Yusuf ya saba wa dokar zabe. Duk da wadannan sakamakon, Gwamna Yusuf ya daukaka kara izuwa kotun koli don neman nasara.

Mutfwang da Goshwe:

A ranar 9 ga watan Janairu, 2024, Kotun Koli ta jingine hukunci a karar da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya shigar, yana kalubalantar kotun daukaka kara ta soke zabensa.

Kwamitin da ya kunshi alkalai biyar, karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ya jingine hukunci bayan sauraron gardama daga bangarorin biyu.

Gwamna Mutfwang, ta bakin lauyansa Kanu Agabi, ya bukaci kotun da ta tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke tare da yin watsi da hukuncin kotun daukaka kara.

Gwamnan ya kara da cewa wadanda suka amsa, Nentawe Goshwe da APC, ba su da ‘yancin yin tambaya kan harkokin cikin gida na jam’iyyar PDP.

Kotun Koli Zata yanke hukuncin jihohi.

Duk da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a watan Nuwamba, Gwamna Mutfwang ya bi sahun kotun koli wajen daukaka kara da nufin samun nasara.

Lawal da Matawalle:

A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.

An ayyana Lawal, wanda ke wakiltar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, inda ya kayar da Bello Matawalle na jam’iyyar APC.

Sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben, Matawalle ya kai karar kotun daukaka kara, inda a ranar Alhamis din da ta gabata ta soke nasarar Lawal tare da ba da umarnin sake gudanar da sabon zabe a wasu yankuna.

Gwamna Lawal dai ya daukaka kara zuwa kotun koli da nufin samun nasara.

Muhammad Abubakar na Bauchi

Haka kuma a watan Nuwamba, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

Kwamitin mutum uku ne ya yi watsi da karar da dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Sadique Abubakar ya shigar.

Duk da hukuncin da kotu ta yanke na goyon bayan Gwamna Mohammed, yanzu maganar tana gaban kotun koli domin yanke hukuncin karshe.

Sanwo-Olu da GRV, Jandor:

A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke na tabbatar da Babajide Sanwo-Olu da Obafemi Hamzat a matsayin gwamna da mataimakin gwamnan jihar Legas.

Kotun dai ta yi watsi da karar da jam’iyyun PDP da LP suka shigar saboda rashin cancanta.

Ba su gamsu da hukuncin ba, ‘yan takarar jam’iyyar LP da PDP sun garzaya kotun koli, inda suke sa ran samun nasara a ranar Juma’a.

Nwifuru da Odii:

A ranar Talata ne kotun koli ta yanke hukunci a karar zaben gwamnan jihar Ebonyi.

A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara da ke Legas ta tabbatar da zaben Francis Nwifuru na APC a matsayin zababben gwamnan jihar Ebonyi, inda ta yi watsi da karar da Chukwuma Odii na PDP ya shigar.

Duk da hukuncin kotun, Chukwuma Odii ya daukaka kara izuwa kotun koli don neman nasara.

~Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG