Shafin Facebook Na Fuskantar Karancin Ziyarar Jama'a

Shafin zumunta na yanar gizo Facebook, na fuskantar koma baya na masu ziyartar shafin a kowace rana, hakan kuma ya faru ne tun gabanin sanarwar da kamfanin yayi na canza tsarin aika labarai kai tsaye a watan Janairu.

Hakan kuma nada alaka da yadda mutane ke aikawa da kananan sakonin bidiyo, da suke daukar hankalin jama’a, shafin ya samu raguwar mutane da kimanin kashi 5% a kowace rana.

Tun a kusan karshen shekarar 2017 shafin ya fara fuskantar matsalar karancin masu ziyara, kamfanin dai ya bayyana cewar duk da raguwar ziyarar mutane babu wani abu da ya canza a yadda shafin ke aiwatar da aikin sa.

Shugaban kamfanin Mr. Mark Zuckerberg, ya bayyana cewar babban burin sa, shine su samar da hanyar da mutane zasu cigaba da tattauna wasu abubuwa masu ma’ana da karuwa a rayuwar su.

Ya ce “Taimakon mutane su gana da ‘yan uwan su shine abu mafi muhimmanci, ba wai la’akari da karancin lokaci da suke yi a kan shafin ba” za kuma su tabbatar da cewar mutane sun samu ganawa da ‘yan uwansu cikin inganci da biyan bukata.