Madina Muktar Dodo ‘yar asalin kwaryar garin Katsina ce, wada ta samu nasarar kammala karatun ta na firamare, da sakandire duk a Najeriya, daga bisani ta halarci Jami’ar ‘Wales Institute Cardiff’ inda ta fara karatun ta na gaba da sakandire, a fannin ‘Business and Humanities’ ta samu nasarar kammala karatun digirinta na farko kuma a fanin ‘Business Information Systems’.
Baya nan ta kara zuwa matakin digiri na biyu inda ta kammala karatun ta a bangaren ‘Management Information systems’ ya zuwa yanzu Madina na zurfafa karatun ta a matakin digirin digirgir a bagaren ‘Information Security.’
Dalilin daya sa Madina ta shiga wannan fannin karatu na zurfin bincike akan ‘Information Security’ shine don taga cewa matsalolin mutane na yau da kullum game da satar bayanai, kudi, sirrin kamfanoni, rushewar kwanciyar hankali da yake-yake da juna da ake aikatawa ta yanar gizo ta ragu.
Ta dukufa wajen gudanar da bincike wanda ta iya gano cewar za’a iya rage matsalolin, idan akayi amfani da wasu hanyoyi da suka hada da yada sanarwa game da mahimmancin bincike a wannan fanni na information security.
Haka kuma matasa na da bukatar zurfafa karatu a wannan fanni, domin a hada kai don magance matsalolin zamba a yanar gizo. A karfafa son karatu kowane iri ne a zukatan matasan maza da mata, domin ba’a san ko wanne zai amfani kasar ba.
Daga karshe ta ja hankalin jama’a wurin kula da irin abubuwan da zasu iya fadi ko rubutawa game da sirrin rayuwar su, a kafofin yada labaru ta yanar gizo, daya daga cikin shawarwarin da Madina taba mata shine, kowane matashi ko matashiya su tashi tsaye wajen neman ilimi a kowane mataki, ga mata kuwa babu inda aure yake hana karatu don haka wannan babbabn kalubale ne ga duk matasa.
Facebook Forum