Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Apple Zai Ba Mutane Masu Tsofaffin Wayar iPhone Dama


Shahararren kamfanin na’urorin zamani na Apple, ya bayyana cewar zai ba ma’abota amfani da tsofaffin wayoyin iPhone damar budewa da kulle, kafar sabunta manhajar wayar su a nan gaba idan kamfanin zai sabunta manhajar.

Damar zata ba mutane masu amfani da tsofaffin wayoyin rufe tsarin, don ba wayoyin su damar aiki cikin sauri, kana da dakile tsarin dake kashe karfin batirin wayar su.

A jiya Laraba kamfanin ya bayyana cewar zai fitar da tsarin sabunta manhajar wayoyin iPhone, wannan tsarin zai ba masu amfani da wayar iPhone damar maido da wayoyinsu suyi aiki cikin gaggawa.

A watan jiya ne kamfanin ya aminta da cewar, tsarin sabunta manhaja da suka fitar a baya na rage karfin saurin wayoyin masu amfani da wayar iPhone, wanda kamfanin ya kara da cewar, tsarin anyi shi ne domin ya kara tsawon shekaru ga tsofaffin wayoyi.

Amma a karshe kamfanin dai ya ba masu amfani da wayar ta iPhone hakuri, kana da daukar alkawalin maye gurbin tsohon batiri da sabo ga duk wanda wayar sa ta kamu da matsalar a kudi kalilan na dallar Amurka $50.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG