Wani dan Najeria, ya sayi wata motar kece raini da ake kira Bugatti Veyron, daga hannun fitaccen dan wasan kwaikwayon nan na Amurka, Arnold Schwarzenegger.
Ya sayi motar akan dalar Amurka miliyan 2.5, kwatankwacin naira miliyan 900 kenan. Mr. Obi Okeke, shaharren dan kasuwa ne mai harkar dillancin motoci da ke zaune a nan Amurka.
A Wani rahoto da mujallar TMZ ta ruwaito, Mr. Okeke na da niyyar siyar da motar, wacce ya saya a hannun Schwarzenegger , wanda tsohon gwamnan jihar Calirfonia ne. Motar ta Bugatti ta yi tafiyar kimanin mil 1,000 ne kawai tun da aka saye ta.
Ta kuma samu shiga cikin kundin tarihin abubuwa ban mamaki na duniya da aka fisani da ‘Guiness World Records’ domin ita ce motar da ta fi kowace mota gudu a fadin duniya da aka kera, wadda ke gudu kilomita 431.072 a kowace sa’a daya, kimanin tafiyar Kaduna zuwa Abuja cikin sa’a daya.
An fi sanin Mr. Okeke da Doctor Bugatti saboda ya siyar da makamanciyar irin wannan motar wa tauraron wassan boxing, Floyd Mayweather, a watan Agustar shekarar da ta gabata.
Mr. Bugati mai shekaru 56, yana aiki a kamfanin motoci masu tsada inda yake siyan motoci kirar Amurka, yana gyara su. Yana harkar motocin da farashinsu na miliyoyin kudi ne, sai ya siyar da su ga duk wanda zai ba shi riba.
Facebook Forum