Kamfanin Facebook ya ce zai rika aika labarai a kan shafufukan masu amfani da shafin, ko da kuwa basu bukaci hakan ba, Kama da ga yau, zamu nuna labarai da abubuwan da ke faruwa a biranen da masu amfani da shafin ke ciki, shugaban kamfanin Mark Zuckerberg, ne ya bayyana sabon canjin da aka samu a kamfanin a wani rubutu da yayi a dandalin na facebook.
Canjin yana nufin mutane dake bin shafukan watsa labarai, zasu iya ganin labarai daga wannan shafin, kuma wadanda basa bi suma zasu ga labaran idan wadanda suke cudanya dasu ko kawance da juna, labaran zasu bayyana a shafufukan su suma.
Mr. Zuckerberg, ya ce yunkurin nasu ya samo asali ne daga yawon da yayi a cikin Amurka, a shekarar da ta gabata, ya rubuta cewa mutane da yawa sun bayyana masa cewar idan zasu dauke hankali daga abubuwa marasa amfani, su maida shi zuwa kan masu amfani, da abubuwan cikin gida, za’a samu ci gaba baki daya.
Facebook Forum