Kamfanin Ford Zai Gwada Mota Mai Tuka Kanta A Shekarar 2018

A shekara mai zuwa kamfanin “Ford Motors” zai kaddamar da sabuwar motar sa mai tuka kanta, ana sa ran gwajin zai fara ne a gari daya, amma ba zai fara kera motocin sayarwa ba sai a shekarar 2021.

Kamfanin ya bayyana cewar zai fara gwajin ta hanyoyi da dama, a wani yunkuri na gano ko akwai wasu matsaloli da motocin zasu iya fuskanta a lokacin tafiya da kansu.

Shugaban kamfanin Mr. Jim Farley, ya rubuta a shafin sha na yanar gizo cewar, kamfanin na Ford zai fara gwajin motocin masu tuka kansu da kansu, kana da lura da yadda mutane ke kai-komo a kan tituna, harma da yadda motocin zasu rika isar da sako akowane lokaci.

Kamfanin GM, ya bayyana cewar a shekarar 2019, zai fara gwajin mota mai tuka kanta, da kuma lura da yadda mu’amala zata kasance tsakanin motocin da mutane, ana sa ran aiwatar da gwajin akan motar su samfurin Chevrolet Bolt.