Facebook ya kaddamar da wata sabuwar manhaja ta kananan yara da ake kira Messenger Kids, wadda zasu iya aikawa abokansu sakonnin kar ta kwana, amma da izinin iyayensu.
Ita dai wannan manhaja an kirkire ta ne domin kananan yara ‘yan kasa da shekaru goma sha uku, wadanda bisa tsakin dokar Facebook ba zasu iya bude shafin kansu ba a kafar sada zumuntar, wanda wasu lokuta su kanyi.
Manhajar Messenger Kids an kirkireta ne ta hanyar baiwa iyaye ikon gudanar da komai. Wanda yaro ba zai iya kara aboki ko goge aboki ba tare da izinin iyayensa ba.
Yayin da kananan yara ke amfani da kafofin sada zumunta da manhajojin aikawa da sakonnin kar ta kwana, da aka kirkiresu domin matasa da manya.
Kristelle Lavalle, kwararre ne masanin halayyar kananan yara, shine ya baiwa Facebook shawarar kirkirar wannan manhaja domin kananan yara.
Facebook Forum