A jiya Litinin kamfanin Facebook, suka bude sabon ofishin su a kasar Burtaniya, wanda suke sa ran nan da sabuwar shekara zasu dauki karin ma’aika 800, kamfanin dai na kokarin cika alwashin su na fadada ressan su a duniya, musamman idan akayi la’akari da halin da kasar ta Ingila ke ciki, na kokarin rabuwa da sauran kasashen turai.
Kamfanin ya kara da cewar, fiye da rabin ma’aikatan su a birnin Landon zasu maida hankali wajen ganin sun kara karfin na’urorin su, wanda suke kokarin zamar da ofishin na birnin Ingila, na biyu a girma bayaga ofishin su na kasar Amurka.
Kuma zasu kaddamar da wani dakin tattara bayanai mai suna LDN-LAB don kokarin habbaka harkar kasuwanci a kasar ta Ingila. A cewar mataimakin shugaban kamfanin Nicola Mendelsohn, kamfanin na Facebook, a shirye suke wajen ganin sun tallafawa tsarin kimiyya da fasaha a kasar ta Burtaniya.
Kasar ta Ingila, kasace da tayi suna a cibiyar kasuwanci, da ta samu lambobin yabo daga kasa-da-kasa, hakan zai taimaka wajen ganin an ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. Domin kuwa kasar na daya daga cikin kasashen da suka taimaka ma kamfanin na Facebook wajen zama abun da ya zama a wannan karnin na 21.
Facebook Forum