Shafin YouTube ya ce zai ‘dauki ‘karin ma’aikata da zasu taimaka wajen rage yawan hotunan bidiyon da suka karya tsarin dokar shafin.
Shugabar YouTube Susan Wojcicki, ta ce “wasu da ba mutanen kirki ba sune suke karuwa a shafin” kafanin Google ne dai ya mallaki shafin YouTube, inda wasu mutane ke amfani da kafar wajen yada karya da yaudara da kuma cutar da mutane.
Susan ta ce a shekara mai zuwa Google zai samar da ma’aikata sama da dubu 10 da zasu duba ire-iren matsalolin da ake fuskanta.
Haka kuma YouTube zai yi amfani da wata fasaha da zata rika bankado hotunan bidiyo ko sharhi da suka kunshi miyagun kalamu, ko wani abu da zai cutar da kananan yara. Yanzu haka dai shafin yana cire duk wasu hotunan bidiyo da suke koyar da tsattsauran ra’ayi.
Shafin YouTube dai na ‘daukar matakan tabbatarwa masu yin talla a shafin cewa, tallarsu ba zata fito kusa da ire-iren gurbatattun bidiyon ba.
Akwai rahotanni da aka fitar dake nuna yadda ake saka wasu hotunan bidiyo don janyo hankulan kananan yara, inda wasu masu cin zarafin kananan yaran ke rubuta sharhi akan ire-iren bidiyon.
Facebook Forum