Batiri na musamman da yafi girma a fadin duniya, ya fara aikin samar da wutar lantarki a karon farko a yankin kudancin kasar Australia. Aikin samar da batirin na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar, da kamfanin kera motoci masu amfani da hasken rana na kasar Amurka Tesla, da kamfanin Neoen, kamfanin wuta na kasar Faransa.
Kimanin watanni uku kenan da suka wuce, kamfanonin suka dauki alwashin samar da irin wannan batirin a karon farko, da zai dinga bada wuta ga tarin jama’a mazauna wani yanki a kasar ta Australia.
Wannan shine batiri na farko da aka taba kirkira a fadin duniya, da yake aiki kamar haka. Yana samar da karfin wuta da ya kai kimanin megawatt 100, karfin batirin zai magance matsalar rashin wuta a yanki.
A watan Satunba da ta gabata, yankin dai sun fuskanci matsalar daukewar wuta, biyo bayan tsawa da iska da aka samu a yankin, hakan yasa mahukunta suka ga akwai bukatar samar da irin wannan batirin, don magance matsalar wuta a gaba.
Jama’ar yankin na kara nuna farincikin su, da kuma mika godiya ga mahukunta, da suka nuna damuwa da irin halin da suka shiga, musamman kamfanoni da suka bada kyautar batirin, don inganta rayuwa a yankunan.
Facebook Forum