Daga wayoyin hannu zuwa motoci, talabijin, da firiji, dama sauran wasu na’urorin zamani, da suke hade da yanar gizo, duk tsarin dake hada wadannan na’urorin ana kiran shi "yanar gizon gama gari" “Internet of things” a turance.
Birnin Los Angels, gari na biyu mafi girma a kasar Amurka, wanda zirga-zirga kan iya zama wani abu mai wuya, saboda kasancewar cinkoso. Musamman idan aka hada da tafiya a mota.
Hakan yasa karamar hukumar birnin suka fito da wani sabon tsari, da zai taimaka wajen rage cinkoso, ganin yadda garin yake zagaye da yanar gizo a kowane bangare.
Idan aka duba wuta mai bada hannu a kan titi, na da yanar gizo, mitocin biyan kudin ajiyar motoci, da yadda motoci ko wayoyin hannun mutane ke dauke da yanar gizo, yasa suke ganin za’a iya inganta amfani da yanar gizon.
Wanda mutun zai iya amfani da wayar shi, don sanin inane ake da wajen ajiyar mota da babu kowa, ta amfani da wata sabuwar manhaja da suka kirkira, haka zata sanar da mutun a duk lokacin da fitila mai bada hannu zata tsayar da mutun.
Shi dai sabon tsarin mutane zasu iya saukar da manhajar a wayar su, kana da bada izini ga manhajar da ta dauki bayanan inda mutun yake, don hadawa da sauran na’urori da suke kusa da mutun masu amfani da yanar gizo.
A duk lokacin da mutun yayi hakan, zai samu duk wani bayani da zai bukata da ya shafi cikin birnin, don sanin yadda mutun zai gabatar da wasu abubuwan shi batare da ya shiga cikin matsalolin gosulo ba.
Facebook Forum