Akwai Alamun Dawo Da Wasu Manhajoji Kan Wayar Apple Bada Jimawa Ba

A shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar China, ta umurci kamfanin Apple da su cire wasu manhajoji a wayar su, musamman wayar da za ayi amfani da ita a kasar ta China.

Kamfanin Apple sun bi umurnin gwamnatin na China, wanda suka cire manhajojin, gwamnatin dai na ganin cewar wadannan manhajojin zasu ba masu amfani da wayar ta Apple damar boye kansu ko yanar gizon da suke amfani da ita.

A duk lokacin da mutun yake amfani da wayar, ba za’a iya gano inda yake ba, da kuma sanin wane irin bayanai yake aikawa, saboda manhajojin suna ba mutun damar boye bayanan shi na sirri.

A jiya Laraba, lokacin da shugaban kamfanin Apple Mr. Tom Cook, yake bayani a kasar ta China, ya bayyanar da cewar akwai alamun za a dawo da manhajojin a kan wayoyin Apple, nan bada jimawa ba.

Ya kara da cewar mutane da dama basu yadda da irin akidojin shiba, na bin umurnin gwamnatin ta China, amma abu da ya sani shine, dole su dinga bin dokokin kasashen da suke mu’amala da su.

Domin kuwa ta haka ne kawai zasu iya samun nasara a kasuwancin su, a ranar Lahadi da yake jawabi a taron kasa-da-kasa na yanar gizo ta duniya, ya bayyanar da cewar, zasu cigaba da matsama gwamnatin China lamba, har sai sun aminta da dawo da wadannan manhajojin, a wayoyin da za'a dinga amfani da su a kasar ta China.

Hakan zai ba 'yan kasar damar bayyanar da bayanai, ko boye duk wani bayani da basu so wani ya gani.