Wata doka ta kungiyar kasashen Turai ta hana Facebook kaddamar da sabuwar manhajar da ya kirkira da zata taimaka wajen gano mutanen da ke da niyyar kashe kansu.
Facebook dai ya sanar da cewa zai yi amfani da wata fasaha wajen gano kalamun ganganci daga mutanen dake tunanin ‘daukar ransu, ta hanyar hoton bidiyo da rubutun da suka kafe a kafar sada zamuntar.
Duk da haka, wata doka dake kare bayanan mutane a kasashen Turai, wadda ta haramta duba ko yin amfani da bayanan mutane ba tare da izininsu ba, na nufin wannan manhaja da Facebook zai kaddamar ba zata samu gurin zama ba a Turai.
Yanzu haka Facebook ya baiwa mutane damar isar da rahoto idan suka yi tunanin wani mutum yana cikin hatsari, wanda a nan ne ma’aikatan Facebook zasu iya aikawa da mutumin lambar da zai kira don samun taimako, ko ankarar da abokan mutumin.
Daga nan ne shugaban Facebook, Mark Zuckerberg, ya sanar da cewa kamfaninsa ya kirkiri manhajar da zata rika zakulo mutanen da ke da niyyar kashe kansu, ta hanyar abubuwan da suke kafewa a shafukansu.
Facebook Forum