Dr. Sani 'Yantandu Uba, dan asalin karamar hukumar Dala ne, a jihar Kano. Ya samu damar kammala karatun shi na matakin firamari da sakandire, duk a mahaifar shi ta jihar ta Kano. Daga bisani ya samu takaddar shaidar koyarwa ta kasa wanda aka fi sani da NCE, a Kwalejin Sa’adatu Rimi ta Kano.
Duk a cikin yunkuri na neman ilimi, ya sami damar ci gaba da karatun shi na digirin farko, a Jami’ar Bayero ta Kano, inda ya karanta B.A Ed English. Bayan yan shekaru kadan, sai ya sami damar zuwa England domin yin digiri na biyu, a fannin ‘Applied Linguistics’ a Jami’ar Leeds. Bayan da ya kammala sai ya koma Najeriya, inda ya canza wajen aiki, zuwa Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Duste a jahar Jigawa.
Bayan da yayi aiki na shekara biyu, da yan watannni sai ya ga akwai bukatar ci gaba da neman ilimi, inda ya sake komawa Jami’ar Leeds dake Birtaniya, wanda ya samu damar kammala karatun shi a matakin digirin digirgir, Ph. D duk a bangaren sanayyar harce daban-daban ‘Applied Linguistics’
Dr. Sani, yana ganin cewar badan ilimi ba, da bai kai inda yake ba a yanzu. Yana ganin cewar babu wata al’umma da zata cigaba batare da ilimi ba, idan akayi la’akari da kasashen da suka cigaba a duniya. Ilimi da bincike suka kai su matakan da suke a yanzu.
Ko dai ta karfin soji, karfin tattalin arziki, dama uwa uba cigaba a fannin kimiyya da fasaha. Duk hakan na samuwa ne idan aka samu al’umma na da ilimi musamman matasa.
Matasa su manta da kayan kyale-kyale na rayuwa da jin dadi, domin sai an sha wuya ake shan dadi “kamar yadda masu iya magana kance”. Saboda shi ilimi hasken rayuwa ne.
Matasa su bar hangen wasu da irin rayuwar da suke gudanarwa mai tsada su nemi ilimi. Ta wannan neman ilimin zasu iya magance matsalolin su na rayuwa da kuma kawo ci gaba mai amfani.