Rahotanni daga Najeriya sun bayyana cewa irin tallafin da ake samarwa a yankunan karkara ya taimaka gaya wajen dakile yawan kaurace kaurace da al’umonin mazauna karkara ke yi zuwa birane da zumar neman kudade wanda a da can baya, ya zama ruwan dare gama duniya a yawancin sassan arewawacin Najeriya.
Yawancin tallafin da ake samu na fitowane daga wajen zababbun wakilai ta hanyar raba kayan koyon sana’a da kuma na’urorin da ake sarrafawa kamar su baburan tukawa da sauransu.
A binciken data gudanar, kungiyar National Youth Development a Najeriya, ta bakin shugaban ta Alhaji Sagir Madakin Shira, ya ce sun fahimci cewa lallai an sami raguwar kwarar jama’a musamman matasa daga karkara zuwa birane domin neman ayyukan yi, lamarin da ke jefa da dama cikin matsala.
Shugaban ya kara da cewa, idan kaba mutumin kauye kudi Naira dubu biyar, ya ishe shi jari, haka mace idan ka bata injin nika, cikin kankanen lokaci zaka ga ta zama mai dogaro da kai.
Domin cikakken bayani, saurari rahoton Muhammed Garba Auwal Daga.
Facebook Forum