Wani gidan tarihin kasar Australia, tare da hadin gwiwar kamfanin IBM kamfani da ya shahara wajen kirkirar na’urar kwamfuta a duniya, suna yunkurin kirkrijar wata manhaja na kidaya.
Ita dai wannan manhajar za’a yi amfani da ita ne wajen kidayar kwadi, wadanda suka kasance kwadi ‘yan asalin kasar ta Australia. Bincike ya tabbbatar da cewar akwai nau’o’i na kwadi a kasar ta Australia, da suka kai kimanin 240.
Manhajar zata taimaka wajen kidayar kwadi a kasar, a cewar manazartan wannan manhajar zata kasance ta farko a duniya, da aka kirkrira, jama’ar kasar zasu taimaka wajen kidayar.
Za’a bukaci kowane dan kasa, da ya saukar da manhajar a wayar shi, a duk lokacin da yaga kwadi sai ya dauki hoton su ta manhajar, hakan zai basu damar sanin baki daya kwadin da ake dasu a cikin kasar.
Da kuma sanin adadin yawan kowane nau’i, na kwadi da ake dasu, amfani da manhajar zata taimaka wajen kidayar, batare da an shiga hakkin kwadin ba. Yanzu haka ana kara samun raguwar kwadi a fadin duniya.
Haka kwadin kasar Australia basu tsira ba, a sanadiyar matsalar dumaman yanayi, da ake kara samu a fadin duniya. A cewar manazartan yawaitar kwadi a kasa, alamu ne dake nuni da cewar akwai yanayi mai lafiya da nagarta a wajen da suke rayuwa.
Facebook Forum