Kamfanin Google ya kwashe ‘yan watanni yana goge duk wasu hotunan bidiyo dake yada ko tallata akidar ta’addanci da tsatstsauran ra’ayi akan shafin YouTube.
Kamar yadda YouTube yace ranar Litinin, anyi wani gagarumin sauyi ga ka’idoji, bayan da suka ‘kara fuskantar matsin lamba daga gwamnatoci.
Sabbin ka’idojin zasu shafi yadda duk wasu hotunan bidiyon da wasu mutane ko kungiyoy da Amurka, ko Birtaniya, suka ayyana a matsayin ta’addanci.
Mai magana da yawun YouTube wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda sha’anin tsaro, ya tabbatar da wannan sababbin sauyin ka’idoji, sai dai kamfanin bai fadi ranar da zai fara aiki ba.
A kwai daruruwan hotunan bidiyon da aka kafe masu cusawa mutane akidar shiga kungiyoyin ta’adda na ‘dan al-Qaida Anwar al-Awlaki, akan Youtube, yana bayar da tarihin musulunci, hotunan bidiyon da aka yi su da dadewa kafin ya fara cusawa mutane akidar kai hari ga Amurka, duk suna daga cikin wadanda aka cire daga dandalin YouTube.
Facebook Forum