Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Iyaye Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Shafukan Yanar Gizo


A yayinda ake cigaba da bayyana alfanun kafofin sada zumuncin zamani a wannan karnin, bisa ga dukkan alamu iyaye da dama na korafi game da yadda irin wadannna shafuka ke zama kalubale ga karatun wasu matasan, kamar kallon hotunan batsa da rashin da'a.

Shafufukan yanar gizo na taka muhimmiyar rawa wajen fadakarwa da ciyar da al’ummah gaba a fadin duniya, kodayake duk da muimmancinsu akwai munanan abubuwan dake tattare da su.

Matasa a kasashe masu tasowa, suna amfani da kafofin ta hanyar da ta dace, wasu lokutan kuma ta gurbatacciyar hanya.

Iyaye da malaman addinai na nuna damuwar su akan yadda shafufukan ke kara gurbata tarbiyyar ‘ya’yan su, ganin cewa shafufukan na ba matasa damar tura sakonni babu shamaki.

Malan Umar Faruk Abdullahi, na daya daga cikin iyayen da ke nuna damuwar su akan wasu fina-finai kamar na batsa da akan sanya a shafufukan yanar gizo, mafi akasarin matasa a wannan zamanin basu rabuwa da kalle-kalle.

Wasu iyaye na ganin cewa amfani da wasu shafukan yanar gizo zai kawo masu cikas, domin kuwa suna iya kokarin su wajen ganin sun tarbiyantar da ‘ya’yansu, ganin cewa kai tsaye yaran na samun damar kallo, da karanta abubuwa marasa amfani ga rayuwar su.

A bangaren matasa kuma, suna ganin cewar ai dama duk wani abu da aka kirkira yana da alfanu da rashin alfanu tattare da shi. Abin da ya fi dacewa shine, matasa su maida hankali wajen amfani da shafufukan don ciyar da rayuwar su gaba.

Su kuma masana na ganin cewar babu wani abu da ba’a samu a shafufukan yanar gizo, musamman idan akayi la’akari da yadda shafufukan suka saukaka bincike, yadda mutane zasu iya amfani da wasu kafofi don ilmantar da kansu dama al’uma baki daya.

Babban abin la’akari anan shine matasa su dage don ganin sun ci gajiyar damar da suke da ita wajen ilimantar da kansu ta hanyar da ta dace, musamman amfani da shafufukan zumunta na zamani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG