Yakamata mawaka sun guji zubar da mutuncin su a bisa sana’ar waka inji wani mawaki Sani Muhammad Abdullahi, wanda akafi sani da Sani Salo.
Yace ba dade bane mawaka su dinga bin ‘yan siyasa ana wulakantasu kamar yadda wasu ke yiwa ‘yan siyasa waka batare da an bukacesu su yiba.
Sani Salo, ya ce shi baya bin bango domin yi wa wani dan siyasa waka kamar yadda wasu mawaka kan yi a yanzu. Ya bayyana haka ne yayi da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, a birnin Kano.
Ya kara da cewa babban makasudin da ya sa shi yin waka shine domin fadakarwa kamar yadda zamani ya canza dole salon wa’azantarwa ma ya canza da zamani.
Ya ce, Allah ke da zamani, a yanzu al'uma su raja’a wajen sauye sauyen zamani saboda haka a cewarsa tilas rawa ya canza idan kida ya canza
Sani Salo kafin waka, rawa ya fara yi daga bisani ya koma ga waka, inda yake cewa babban burinsa kamar kowanne mawaki ya samu daukaka sannan wakokinsa suyi tasiri a tsakanin alummarsa.
Facebook Forum