Zainab Kaita: Gudun Mawar 'Yan Najeriya A Kimiyyar Magunguna A Duniya Bata Misaltuwa

Zainab Abdulaziz Kaita

Zainab Abdulaziz Kaita, daliba dake karatun digirin farko a jami’ar ‘Gulf Medical’ dake kasar Dubai a daular Larabawa. Tana zurfafa karatun ta a kimiyar hade-haden magunguna ‘Doctor of Pharmacy’ a turance.

Babban abun da ya bata sha’awar karatun aikin hada magani, shine yadda a Najeriya, babu mata da yawa da suke wannan karatun. Ganin yadda kuma aikin yake da matukar muhimanci ga rayuwar dan adam. Duk wadannan suna daga cikin abubuwan da suka sa take karatun sanin yadda ake hada magani.

Wani babban kalubale da matakan kan fuskanta, musamman idan sukaje asibiti, kana akace likita namiji zai dubasu, sukan zama basu samun damar iya bayyanar da abun dake damunsu da gamsarwa. Wannan ba karamin koma baya yake haifarwa ga al’umma ba, don haka akwai bukatar mata da yawa su shiga wadannan karatun, don taimakawa wajen magance wannan matsalar.

Haka da yawa ‘yan mata da suka kammala karatun sakandire, su kan maida hankalin su kawai a wajen aure, batare da kokarin samun hanyar da zasu taimaka ma kansu koda kuwa a gidan auren ne.

Hakan shima wani babban kalubale ne, ilimin ‘ya mace ilimi ne da yake gamsar da duniya, domin kuwa tana haihuwa ne tana kara tarbiyantar da abunda ta haifa. A she kuwa tahaka ake samun al’uma nagartacciya.

Iyaye akwai bukatar su kara bama ‘yayan su, musamman mata kwarin gwiwar neman ilimi a kowane mataki. Hakan zai taimaka a warkar da cutar da ta dade tana yawo a cikin jama’a musamman a Arewacin Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Zainab Kaita Daliba Mai Karatun Kimiyar Maggunguna '3:45"