Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Basirar Matasa A Fadin Duniya, Shafin Facebook Ke Tunkaho Da


Kamfanin shafin zumunta na Facebook, na bada dama ga matasa, ba kawai sada zumunci a shafin ba, harma da damar tsara rayuwa tun da kananan shekaru. Daya daga cikin ire-iren damamakin da kamfanin kan bayar, sun hada da irin wannan taron da aka gabatar na matasa a fadin duniya mai take F8.

Matasa a ko’ina a fadin duniya sun halarci taron, don nuna irin tasu hazakar. Daya daga cikin matasa Khailee Ng, da suka halarci taron, ya bada nashi labarin ta yadda ya fara, yace a ‘yan shekarun baya bashi da aikin yi, wanda ya wuce sata, a lokacin da ya shiga wani shago ya saci wata riga, sai aka kama shi, daga nan ya daukar ma kanshi alkawalin cewar, zai yi amfani da rayuwar shi ta yadda ya kamata.

Daga nan ya fara kirkirar shafin siye da siyarwa a yanar gizo, hakan yasa mutane suka fara zuwa wajen shi, don ya tsara musu nasu shafin, wajen tallata hajojin su. Daga nan ya fara, zuwa yanzu yana daya daga cikin matasa masu kudi a kasar Malaysia.

Kimanin sama da matasa 4,000 a fadin duniya, suka halarci wannan taron, wanda kowa ya bayyanar da irin tashi fasahar ta yadda za’a inganta shafin zumunta na facebook. Daga ciki babban abun ban sha’awa shine, yadda kowane matashi yazo da irin tashi basirar daban da ta wani.

Matasa a ko ina a fadin duniya, ya kamata su fara amfani da kafofin sadarwar zamani, wajen kirkirar abubuwa da nuna hazakar su a shafufukan yanar gizo, donmin ta nan ne mutane da dama suke binciken masu basira da zummar daukar aiki a manyan-manyan kamfanoni a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG