Babban abin da ke ci mana tuwo a kwarya shine yadda bama samun goyon baya daga wuren manyan mawaka da suka yi sura a harkar waka inji Shamsudeen Adamu Aliyu, wanda aka fi sani da Dan Mama Danko.
Matashin mawaki ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA a yau inda ya bayyana cewa an barsu a baya a harkar waka ba kamar yadda waka take ba a kudu, inda manyan mawaka ke tallafawa masu tasowa domin su sami karbuwa a masanaantar.
Ya ce ya fara waka ne tun yana dan karami yayin da suke kasidu a makarantun islamiyya inda ya koma yana yin wakokin fadakarwa da kuma zamtakewa da soyayya. Shamsu ya ce yana isar da sakonnin ne ta hanyar waka a cewarsa ita ce hanya mafi sauki da zai iya isar da sakonnin sa.
Daga karshe ya kara da cewa babban burinsa shine yayi fice duniya ta sanshi sannan ya goga da manyan mawaka a nan gida da ma kasa baki daya.