Shafin zumunta na Facebook, sun bada tabbacin cewar sun dakile shafufukan dubban mutane a kasar Birtaniya, gabanin zaben kasar da za’a gabatar a ranar 8 ga watan gobe idan Allah ya kai rai.
Kamfanin sun kara daukar kwararan matakai, a kan kamfanonin jaridun kasar, wanda suke kara jawo hankalin jama’a da su dinga duba tushen labari da kuma duba ga shafin da labarin ya fito.
Kamfanin sun kara da cewar, zuwa yanzu suna kara inganta shafin nasu, wajen gano labaran da basu da tushe. A cewar Mr. Simon Milner, shugaban sashen gyare-gyare na kamfanin facebook, suna kara inganta shafin su, kuma sun samu goyon bayan wasu kamfanoni don yaki da wannan matsalar.
Domin ga banin wannan zaben, akwai bukatar magance duk wata hanya da za’a dinga yada labarai da bana gaskiya ba. Yace kamfanin facebook na iya bakin kokarin shi, wajen ganin sun shawo kan wannan babbar matsalar.