Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Najeriya An Gina Gidan Farko Da Gorar Ruwa A Nahiyar Afrika


Gidan Gora
Gidan Gora

An kaddamar da gidan farko da aka gina da gorar ruwa a nahiyar Afrika, taron wasu matasa masu yunkurin kawo karshen dumamar yanayi, da ake samu a duniya. Sun fito da wata fasaha tasu, inda suke gina wani gida, da gorar ruwa da akanyi amfani da su, sai a zubar batare da duba ga wasu abubuwa ba.

Kungiyar matasan mai suna ‘Developmental Association for Renewable Energy’ dake da mazauni a garin Kaduna, sun gina wannan gidan ne a garin Yalwa, dake kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

A ta bakin shugaban kungiyar Malan Yahaya Ahmed, lokacin da yake zagayawa da manema labarai don ganema ido, yadda aikin ke gudana, yace al’uma basa amfani da duk wata dama da suke da, wajen mai-maita amfani da duk wasu abubuwan amfani a rayuwar yau da kullun.

Yace babu wani abu na rayuwar ayu da kullun, da mutane baza su iya sauya hanyoyin amfani da suba, amma da yawa za’a ga mutane basa amfani da ilimin su wajen samar da aikin yi ga matasa da wasa kwakwalwar su.

Ya kara da cewar wannan gidan da suka gina, da gorar ruwa yafi nagarta da gidan da aka gina da bulo, da kimanin kashi 20. Yace gidan gora yana iya zama sama da shekaru 200, idan an yi shi cikin natsuwa da nagarta.

Haka kuma gidan baya kamawa da wuta, kuma bindiga bata ratsa shi, haka girgizan kasa ma bata yimishi komai, bugu da kari gidan na iya jurewa duk yanayi.

Shi dai tsarin ginin gidan gora, ana iya yin shi a ko ina koda kuwa cikin ruwa ne, babban abun dubawa shine yadda aka tsara tushen gidan. Yace ana gina gidan da gorori masu yawa, inda ake zuba musu kasa tare da siminti.

Ya kara da cewar, suna fahariya da wannan yunkurin nasu, don ganin an rage shara a cikin jama’a, kana da samar da aikin yi ga matasa, uwa uba kuwa amfani da basirar su wajen juya tunanin duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG