Dokokin Wasu Jihohi A Kasar Amurka, Nada Ban Dariya Da Al'ajabi!

Tutar Kasar Amurka

Kasar Amurka, kasace daya da keda tsare-tsare masu kama da tsare-tsaren wasu nahiyoyi. A kasar Amurka kadai ne akanyi dokokin kasa, da gwamnatin tarayya ke shatawa, amma gwamnatocin jihohi nada hurumin kin bin dokokin, suna iya samar da nasu dokokin, wanda sukayi dai-dai da mutanen jihar.

Wasu kadan daga cikin dokoki da ake da su a wasu jihohi, amma a wasu jihohi ba’a amfani dasu. A jihar Arkansas, karya doga ne mutun yaje gidan abinci ya danna hone, na mota ko mashin, don hakan zai iya ba mutane tsoro. A jihar California, haramun ne mutun yayi amfani da leda don daukar cefane ko saka duk wasu abubuwa.

A jihar Colorado, kuwa an haramta ajiye kujeru a harabar gida, Su kuwa a jihar Florida, ana biyan kudin ajiyar dabbobi, kamar su doki, rakumi, giwa. Kamar yadda ake biyan kudin ajiyar mota a kan tituna. A jihar Georgia, kuwa karya doka ne mutun ya shiga jirgin ruwa har na tsawon kwanki talatin.

Jihar Hawaii, kuwa karya doka ne mutun ya saka kudi a kunne, a jihar Indiana kuwa haramun ne mutun ya hau kan doki da tsayin shi yakai mita goma. Su kuwa a jihar Kansas, haramun ne mutun ya ci tayar mota. A jihar Kentucky kuwa, babban laifi ne mutun yayi aure fiye da sau uku a rayuwar shi.

A tsarin dokokin wadannan jihohin, idan aka samu mutun da karya daya daga cikin dokokin za’a hukunta shi, wanda zai iya biyan tara ko kuma zuwa gidan kasu, dai-dai da dokar da ya karya.