Kunkuru mai shekaru goma sha biyar 15, a duniya, ya haddasa gobara da ta lakume gidaje, an kiyasta gobarar tayi sanadiyar hasarar kudi sama da dallar Amurka dubu dari da hamsin $150,000 kimanin naira milliyan saba’in da biyu.
Shi dai wannan kunkurun, ana ajiye da shi a wani gida, wanda mai gidan yake ajiye da shi a matsayin nau’o’in dabbobi abun so. A tabakin masoyin kunkurun, kuma wanda yake rike da shi har na tsawon shekaru da dama.
Yace wannan wani tsautsayi ne, domin kunkurun ya gogi wata na’urar dumama daki, da aka saka mishi a cikin dakin shi na katako, wanda hakan ya haddasa tashin gobarar. Gobarar dai har ta shafi rabin gidan makota.
Kunkurun dai ya kone kadan a jikin kokon bayan shi, mutumin mai kunkurun baiyi watawata ba, ya kira kamfanin inshoran gidaje, don bincike da biyan shi asarar da kunkurun shi ya jawo, haka da biyan makotan shi.
Hukumomi a karamar hukumar San Antonio, suna cigaba da bincike dangane da matsalar.