Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tsammanin Kamfanin Yahoo, Na Iya Samu Sabon Suna!


Tambarin Kamfanin Yahoo.
Tambarin Kamfanin Yahoo.

Wani bangare na kamfanin Yahoo, zai samu sabon suna, wanda za a rika kiranshi da Albata. Ana dai iya cewa kamfanin yanar gizo na Yahoo, na amfani da sunan da yayi a shekarun baya. Wanda ta kai ga cewa yana kokarin fansar da wani bangaren kamfanin.

A lokacin da kamfanin Verizon, suka aminta da cewar zasu saye wani bangare na kamfanin, akan kudi dallar Amurka billiyan hudu da milliyan takwas $4.8B, a watan Yuni. Sun cinma matsayar siyan bangaren kasuwanci na kamfanin na Yahoo.

anda suka hada da bangaren aika sakonnin email, bangaren wasanin, da wasu manhajojin kamfanin. Shahararren kamfanin kasar China, na Alibaba shi yake kokarin mallakar sauran, abinda ya rage daga kamfanin. Ana sa ran idan cinikayyar ta kankama, kamfanin zai samu canjin suna daga Yahoo zuwa “Altaba” wannan bayanin ya fitone a bayan taron kusoshin kamfanin a shekaranjiya Litinin.

Ana dai sa ran kammala wannan yarjejeniyar, nan da karshen watan Maris. Ma’anar sunan kamfanin Altaba na nufin Alternative da Alibaba, a cewar wani masani abinda ke kaiwa ya komo, a harkokin kamfanunnuka wanda bai bayyana sunansa ba, sakamamkon rashin samun izinin yin magana akan abinda ya shafi canjin sunan kamfanin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG