Abdulaziz Zubairu Goni, matashi dan asalin jihar Adamawa, daga karamar hukumar Mubi ta Arewa. Wanda ya samu damar kammala makarantun firamari da sakandire, haka daga bisani ya shiga jami’ar Maiduguri, inda ya karanci lissafi “Mathematics” a turance.
Abdulaziz, yayi bautar kasa a makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Nasarawa a garin Lafia. Bayan ya Kammala aikin bautar kasa, ya samu aiki a makarantar “Nigeria Ghana International College” dake Abuja. Ya samu damar karo karatu a matakin digiri na biyu, a Jami’ar “Technique University” dake garin “Kaiserslautern” dake kasar Germany.
A yayin karatun shi na jami’a, ya koyi sana’ar gyaran kwanfuta, wanda yayi amfani da baiwar da Allah, yayi mishi wajen gyaran kwanfutar, don samar ma kanshi aikin yi. Hakan yasa ya tara kudi da yayi amfani da su wajen biya ma kanshi kudin makaranta a kasar Germany.
Yana da tabbacin cewar babu maraya sai raggo, domin kuwa bashi da wanda yake taimaka mishi a rayuwa, don ya dogara da kan shi, hakan ya bashi damar kaiwa ga abun da yake yima kanshi sha’awa a rayuwa. Na samun ilimi ba kawai a kasar Najeriya ba, harma da fita kasar waje.
Ya zuwa yanzu yana kokarin kammala karatun digiri na biyu, a kasar Germany, bisa kokari da hazaka da ya nuna a yayin karatun shi, yasa shi a jerin masu kokari da suke sa ran samun gurbin karatu na matakin diririn digirgi, duk a kasar ta Germany.
Shawarar shi ga matasa a ko’ina musamman na Arewancin Najeriya a yau, shine matasa su tashi tseye wjen neman ilimi, domin kuwa shi ilimi yana da matukar mahimmanci ga rayuwan dan adam a kowane lokaci. Yawancin kasashen da suka ci gaba a duniya, sunci gabane ta hanyar ilimin kimiya da fasaha. Don haka ya zama dole matasa su koma makaranta, suyi karatu domin taimakon kansu da cigaban kasan.