Hukumomi a yankin gabashin kasar China, na wani yunkuri don ganin an rage tsadar sadakin aure. Dalilin kuwa shine, tsadar aure na zama sanadi da ya kesa matasa basa iya aure. Musamman a yankunan karkara, samari basu iya biyan sadaki ga ‘yan-matan su. Haka ‘yan-mata basa bukatar samari da ba zasu iya kashe kudi don fitar da su kunya, a tsakanin kawayen su.
Mafi karancin sadaki kan fara daga Yan kudin kasar China, dubu dari, kimanin naira milliyan hudu da dubu dari biyar. Hakan yasa ba kowane matashi zai iya biyan kudin ba, don haka ayyukan asha na kara habaka a tsakanin mata da maza.
Hukumomi a karamar hukumar Taiqian, na ganin cewar akwai bukatar yanke adadin sadaki, da ba zai wuce Yan dubu sittin ba, hakan zai bama matasa damar iya biyan sadaki, da daukar dawainiyar bukukuwan aure.
Babu wani hukunci da za’a daura ma duk wanda bai bi dokar ba, amma ana kara jan hankalin masu sana’ar shirye-shiryen buki, da su bada hadin kai wajen cinma wannan nasarar. Mutane da dama na bayyanar da ra’ayoyin su, a kafofin sadarwar zamani, kan cewar gwamnati bata da hurumin kayyadema, mutane abun da zasu biya ga masoyan su, abu ne da ya kamata ace masoya da iyayen su ya shafa.