Kamfanin Facebook ya sanar da cewa zai kaddamar da wani sabon shiri kan aikin jarida, a kokarin kamfanin na kawo canji game da yadda gidajen jaridu ke amfani da kafafen sada zumunci.
Wannan yunkuri na Facebook na zuwa ne biyo bayan alkawarin da kamfanin yayi a farkon shekarar nan, kan cewar zai tashi tsaye don dakile yadda ake yada labarun ‘karya a dandalin.
A wata sanarwa da kamfanin ya kafe a yanar gizo, Facebook yace zai yi aiki tare da manyan kamfanonin yada labarai na duniya don samar da sahihiyar hanyar fitar da labaru.
Cikin muradun da Facebook ke fatan ya cimma a wannan shiri kan aikin jarida, sun hada da sabuwar hanyar da kamfanonin yada labarai zasu ke amfani da ita da kuma yadda mutane zasu ke samun sahihan labarai. Shirin dai wani yunkurin ne kan alkawarin da Facebook ya dauka cikin shekarar da ta gabata, na yaki da yada labarun karya a shafukan sada zumunta.