Kamfanin Apple Sun Kara Dankon Soyayya Tsakanin Masoya A Duniya!

Kamfanin Apple.

Bincike ya tabbatar da cewar, a karshen shekarar 2016, mafi akasarin kyaututtuka da aka bayar a lokacin bukukuwan karshen shekara, abubuwan kimiyya da fasaha na kamfanin Apple su, aka bayar kyauta fiye da duk wani abu. Bisa ga al’ada a kasashen Turai, a duk karshen shekara akan bada kyaututuka fiye da kowane lokaci na shekara.

Hakan yayi dai-dai da lokacin bukin kirsimeti, da kokarin shiga sabuwar shekara. Iyaye, masoya, abokai, da ma sauran dangi kan siya abubuwa don bama masoyan su a yayin wadannan shagulgulan bukin. Kamfanin “Firm Flurry” wanda ya gabatar da bincike, ya bayyanar da cewar kayan kamfanin Apple, su akafi badawa kyauta, da kashi arba’in da hudu 44%.

Sai kayan kamfanin Samsung, da suka zo na biyu da kashi ashirin da daya 21%, kana kayan kamfanin Huawei, haka kayan kamfanin LG, sun ci kasuwa, a karshe kuwa sai kayan kamfanin Amazon. Duk dai da cewar kamfanin Samsung sun yi kiranye na sabuwar wayar su ta Galaxy Note 7, wadda aka samu tana da wasu matsaloli.

Babban abun mamaki shine, babu kayan kamfanin Google, a cikin sahun kayan da su kayi kasuwa a wannan shekarar, duk da yunkurin suna samar da sababbin wayoyin Pixel da Pixel XL.