Hukumar kasashen Turai “European Commission” na tuhumar kamfanin facebook, da fitar da wani rahoto da bashi da inganci. Tun a shekarar 2014 ne kamfanin facebook dai ya siye kamfanin Whatsapp, a wannan lokacin kamfanin bai bayyanar da gaskiyar magana a tsakanin yarjejeniyar dake tsakanin kamfanonin biyu ba.
Kamfanin facebook dai sun siya kamfanin a kan kudi dallar Amurka dala billiyan ashirin da biyu $22B. Hakan zai iya sa a ci kamfanin tara da ta kai kimanin kashi daya na yawan kudin da suka siya kamfanin whatsapp.
Hukumar dai ta bayyana yadda suke sa idon akan kamfanonin kasashen waje, da suke taka hakkin bil’adam a kasashen su, a ‘yan kwanakin baya ne dai kamfanin suka ci tarar kamfanin Apple dalla biyina goma sha hudu $14B, haka da kamfanin Goggle, biyo bayan abun da suka kira cin zarafin kasuwa da kamfanin yayi.
Kamfanin dai sun dauki alkawalin boye bayanan mutane, da kawai su kace zasu gabatar da bayanan kawai ga kamfanin facebook, amma sai ga akasarin hakan. Duk dai da cewar da kamfanin su kayi, na baza su hada shafin facebook da na whatsapp ba, sun kasa rike wannan alkawalin.
Yanzu haka dai kamfanin na facebook, suna da har zuwa karshen watan gobe kamin su gabatar da kansu don tattauna wannan matsalar.