Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwaggon Biri Mafi Tsawon Rai A Duniya Ta Cika Shekaru 60!


Gwaggon Biri Colo
Gwaggon Biri Colo

Gwaggon Biri mafi yawan shekaru a fadin duniya, ta cika shekaru sittin 60, da haihuwa. Ita dai wannan gwaggon birin, an haife ta a gidan Zoo dake garin Columbus, na jihar Ohio, a nan kasar Amurka, kimanin shekaru sittin 60, da suka gabata.

Tun bayan haihuwar ta an saka mata suna “Colo” kasancewar itace gwaggon biri, da ta kwashe tsawon shekarun nan a kulle a gidan Zoo. Ta haifi ‘ya’ya uku, kuma tana da jikoki gomasha shida 16, da tattaba kunne goma sha biyu 12.

A ‘yan kwanakin baya ne, aka gabatar da wani aiki a kwakwalwar Colo, amma dai zuwa yanzu likitocin ta, sun tabbatar da cewar tana cikin koashin lafiya. Ma’aikatan gidan Zoo din sun shirya ma gwaggon biri Colo bukin murnar zagayowar ranar haihuwar ta “Birthday” wanda akayi Kek da Apple da Tumatur.

An dai kawata dakin ta da fitilu da abubuwan ban sha’awa, duk don karrama ta a wannan lokaci mai matukar muhimanci gareta. Abun dai da ban mamaki a samu gwanggon biri da ya kwashe yawan wadannan shekarun, duk dai da cewar a jihar Atlanta, suna da wani gwaggon biri Ozzie, mai shekaru hamsin da biyar 55.

A cewar wani gwararren likitina dabbobi, yace suma wadannan dabbobin, suna da wasu nau’I na hallita da yake kama da na mutun, wanda idan mutun ya tsufa za’aga kuzarin shi ya rage, haka zalika suma suna samun raguwar karfin jiki idan shekarun su suka ja.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG