Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanayin Hunturu Ya Hana Sarauniyar Ingila Zuwa Majami'a A Karon Farko!


Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II
Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II

Hunturu mai tsanani ya hana sarauniyar Ingila “Queen Elizabeth II” zuwa majami’a don gabatar da addu’ar bukin Kirismas na wannan shekarar. Kimanin shekara da shekaru kenan sarauniyar bata taba kuskuren rashin zuwa majami’ar ba a irin wannan ranar mai muhimaci.

Rahotanni daga fadar sarauniyar, sun bayyanar da cewar, sarauniyar bata samu zuwa majami'ar ba, bisa dalilin mura da take fama da ita, a duk shekara sarauniyar da iyalanta sukan je majami'ar don gabatar da addu’o’I, amma a wannan karon sai mijinta, ‘ya’yan ta da jikokin ta suka halarci majami’ar.

Sarauniyar mai shekaru casa’in 90, a duniya, da mijinta mai shekaru casa’in da biyar 95, suna kokarin ajiye wasu ayyukan su na sarautar kasa mai dinbin tarihi a fadin duniya, Ingila. Nan ba da jimawa ba, duk dai da cewar ba a bayyanar da zuwa yaushe suke sa ran yin hakan ba.

Dan sarauniyar Yarima Charles, da matar shi da ‘ya’yan su biyu sun isa garin Bucklebury, a yankin yamma na kasar Birtaniya, don gabatar da bukin Kirsmas da dangin matar shi Kate.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG