Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Zai Cika Shekaru 10, Ya Kuma Wayoyin iPhone Suka Canza Duniya!


Kamfanin Apple
Kamfanin Apple

A ranar tara 9, ga watan Janairu na shekara mai zuwa ne, idan Allah ya kai rai ake sa ran shahararren kamfanin Apple, zasu fitar da wata sanarwa ta musamman. Biyo bayan kwashe shekaru goma da kamfanin ya canza duniyar kimiya da fasaha. Kamfanin Apple dai na daya daga cikin kamfanoni a duniya da suka shahara a harkar kimmiyya.

Ana dai sa rai a ranar ne kamfani, zasu bayyanar da wani sabon salon tattalin arziki a fadin duniya. Duk dai da cewar yanzu haka akwai kamfanoni da yawa a fadin duniya, da kan saci fasahar kamfani, wajen samar da waya mai dauke da sunan iPhone, amma kamfanin dai sun kara tabbatar da cewar, kama da wane bata wane, wayoyin kamfanin Apple sun banbanta da na saura, a wajen samar da tsaro da duk wasu abubuwan zamani masu inganci.

Kamfanin dai sun kara da cewar shugaban kamfanin yayi kokari matuka Mr. Steven Jobs, wajen kai kamfanin matakin da yake yanzu a fadin duniya. Suna kara kira ga abokan hurdar su, da su tabbatar da cewar basu siya wayar da aka kirkira daga wani kamfani da sunan su ba.

Idan mutane na bukatar waya mai dauke da makaman kariya ga duk wata barazana, da ‘yan-kutse kan haddasa, to sai sun tashi tsaye wajen tantance wayar kamfanin ta gaskiya, a yayin siyan waya. Kamfanin dai zai cika shekaru goma da kirkira idan Allah ya kai rai cikin shekarar 2017.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG