Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci A Kasar Amurka, Sun Samu Nasarar Dasa Mahaifa Ga 'Yan-Mata 4!


Hallitar Mahaifa A Jikin Mace
Hallitar Mahaifa A Jikin Mace

Taron wasu kwararrun likitoci a kasar Amurka, a karon farko sun gabatar da wani aikin tiyata, ga wasu ‘yan-mata hudu. Su dai wadannan ‘yan-matan an haife su basu da mahaifa. Likitocin dai sun cire mahaifar wasu mata don dasa su a jikin wadannan ‘yan-matan a karon farko a nan kasar Amurka.

An gudanar da wannan aikin ne a Asibitin koyarwa na jami’ar Baylor dake garin Dallas. An samu nasarar kammala aikin a tsakanin ‘yan-matan hudu, sai dai uku daga cikin, sun fuskanci masu matsaloli, da suka shafi gudanar jinni a jikin su, amma daya daga cikin su, ta mike garau.

A tabakin jagoran likitocin Dr. Giuliano, wannan ba wani bakon abu bane a duniya likitanci, na ayi aiki ga marasa lafiya wasu suyi nasara wasu kuma a samu wasu matsaloli. Su dai matan da suka bada kyautar mahaifar tasu, basu da wata alaka da wadanda aka ba.

Wannan wani abune na taimako da su kayi, don bama wasu damar samun ‘ya’ya a duniya. Shekarun ‘yan-matan da aka sakama sabuwar mahaifar, sun fara daga ashirin 20, zuwa talatin da biyar 35 ne. Su kuma masu badawan shekarun su daga talatin da biyar 35, zuwa hansin 50.

A tabakin ‘yan-matan da suka karbi kyautar mahaifar “gaskiya muna cike da farinciki, domin kuwa yanzu zamu samu damar zama iyaye a rayuwar mu ta duniya”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG