Miji Na Yana Yawaita Duka Na Da 'Ya'ya Na - Inji Theresa Mwafu

Madam Theresa Mwafu, kenan mai ‘ya’ya hudu, wadda mai gidanta ke cin zarafinta a duk lokacin da suka sami rashin fahimta.

Ta ce a shekaru takwas da suka yi tare da mai gidanta, rashin jituwa ta fi yawa, kuma har ila yau yana yawaita dukanta da tsangwamarta a yawancin lokuta.

Cin zarafin dan adam, abu ne dake faruwa tsakanin jama’a misali, tsakanin ma’aurata ko tsakanin jami’an tsaro da wanda ake tuhuma da aikata laifi ko kuma tsakanin uwa da ‘yayan riko.

A sakon kwamishinan kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce, lokaci yayi da dukkanin al’umma zasu tashi domin dakile matsalolin cin zarafin dan adam, domin kawo sauyin da ake bukata a duniya.

Akan wannan batu ne wakiliyar dandalinVOA ta tuntubi Shugabar arewa maso yammacin kasar ta hukumar kare hakkin dan adama ta kasa baristar Hauwa Salihu Jauro, inda ta bayyana cewa a wannan shekarar sun sami korafe-korafe kimanin 565, wadanda galibinsu nada alaka da batutuwan cin zarafi tsakanin ma’aurata.

Ga cikkakiyar hirar.

Your browser doesn’t support HTML5

Miji Na a Yawaita Duka Na Da 'Ya'ya Na - Inji Theresa Mwafu