Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakatar Da Gina "Film Village" Ya Katsewa Dubban Matasa Samun Damar Ayyukan Yi - Inji Isa Adamu


Isa Adamu, Madadi
Isa Adamu, Madadi

An bayyana soke dandalin fina finai wato ‘film village’ kuma lamarin bai yiwa masu harkar fim dadi ba, a cewarsa an katsewa dubban matasa damar samun ayyukan yi, batare da la’akari da alfanu ko akasin hakan ga ‘yan masana’antar Kannywood da ma gwamnati ba.

Isa Adamu wanda ak fi sani da Madadi, shi ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da wakiliyar DandalinVOA.

Malamin ya bayyana cewa babban abin sha’awa a harkar fim shine yadda kafin ya shiga harkar yake gani a wasu fina-finai mussamam na ban tausayi ko abin takaici yadda jaruman ke yi tamkar da gaske, sai da ya shigo harkar sa’an nan ya fahimcin cewar duk hanyace ta fadakarwa.

Madadi ya ce gwamnati bata lura da dimbin asarar da ta yi ba, ko ba komai ta rasa dubban kudaden shiga da an gina alkaryar fim village.

Isa Adamu wanda aka fi sani da madadi, mai bada haske a yayin da ake daukar bidiyo wato light man, wanda ya shafe shekaru goma yana masana’atar kannywood.

Me nene dalilin da sa ya fadi hakan- ku saurari cikakkiyar hirar domin jin yadda ta kaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:06 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG